Akalla mutane hudu ne suka mutu bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress na ‘yan majalisar wakilai da na majalisun tarayya ya barke a yankin Igando da ke jihar Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 27 ga watan Mayu, a sakatariyar majalisar Igando-Ikotun da kuma Mosan-Okunola wadda ita ce wurin da za a gudanar da zaben fidda gwani.
A cikin faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo, an ga wasu ‘yan baranda da ke rike da makamai suna fuskantar juna kafin jami’an tsaro su shiga tsakani.
An bayyana biyu daga cikin wadanda aka kashen Surry Boxer da Ogunlaye. Kalli bidiyo daga wurin da ke ƙasa....
Rubuta ra ayin ka