Wata babbar kotun jihar Legas a ranar Juma'a, ya yankewa wani bature dan kasar Denmark, Dane Peter Nielsen, hukuncin kisa bisa laifin kashe matarsa 'yar Najeriya da diyarsa.
Alkali Bolanle Okikiolu-Ighile ya yankewa Dane hukuncin kisan ta hantar rataya ne sakamakon shari'ar da akayi wanda gwamnatin jihar Legas ta shigar kansa. Kamfanin dillancin labarai NAN ta bayyana.
An tuhumi Dane da laifin kashe matarsa mai suna Zainab, da diyarsu yar shekara uku mai suna Petra, a jihar Legas.
Gwamnatin jihar tace Dane ya hallaka Zainab da Petra ne misalin karfe 3:45 na dare cikin gida mai lamba No. 4, Flat 17, Bella Vista Tower, Banana Island, Ikoyi, jihar Lagos.
An gurfanar da shi ranar 13 ga Yuni, 2018.
Rubuta ra ayin ka