Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano sun rike farfesan da ya kai kudin fansa


Daily Trust ta rahoto cewa, hakimin Karfi da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, Abdulyahyah Ilo da aka sace ya samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Masu garkuwan, sun rike karamin farfesa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU), Wudil, Huzaifa Karfi, wanda rahotanni suka ce ya je ne domin kai kudin fansa.

Rahoton The Guardian ya ruwaito cewa ‘yan bindigan sun kashe mutane shida da suka yi kokarin ceto basaraken kauyen a lokacin da suka yi awon gaba da shi.

An ce sun mamaye kauyen ne a kan babura uku daga jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jigawa

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad ya tabbatar da sakin basaraken da masu garkuwa da mutane suka yi.

Ya bayyana cewa mafarauta da ’yan banga sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a cikin daji da ke da nasaba da sace-sace a kauyen Karfi.

A cewar majiya:

“Sun karbi kudin fansa tare da tsare Dr Huzaifa saboda da mutumin da ‘yan banga suka kama. Sun bukaci a sako mutumin nasu a matsayin sharadin sakinsa.”

Wani dan uwa ga sarkin gargajiyan, Yusuf Ismail ya tabbatar da cewa an sako basaraken kuma yana jinya a asibiti.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin ba da bayani idan ya samu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN