An yanke wa wani yaro dan shekara 19 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe kaninsa mai shekaru biyar a Kano.


An yankewa wani matashi dan shekara 19 a Kano, Ibrahim Khalil hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe dan uwansa Ahmad Ado mai shekaru biyar, ta hanyar daure masa hanci da baki.

Mai shari’a Usman Na'abba wanda ya jagoranci shari’ar a babbar kotun jihar Kano, ya yanke wa Khalil hukuncin laifuka biyu da suka hada da garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

Yayin da ya yanke hukuncin daurin shekaru 14 a gidan kaso kan wanda ake tuhuma da laifin yin garkuwa da shi, ya yanke masa hukuncin kisa bisa laifin kisan kai bayan da ya yanke hukuncin cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da karar su ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan Lauyan masu shigar da kara, Mista Lamido Sorondinki ya sanar da kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a shekarar 2019 a Karkasara Quarters a cikin birnin Kano.

Sorondinki ya ce Khalil ya yi garkuwa da dan ‘yar uwarsa mai suna Ado, kuma ana cikin haka ne ya yi amfani da wata soletape ya rufe masa hanci da hanci, kafin a binne shi a wani kabari mara zurfi a Sabuwar Sheka a Kano.

Masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu uku da baje koli hudu a gaban kotu a lokacin da ake shari’ar. 

Ko da yake Khalil ya musanta cewa yana da hannu a cikin mutuwar dan uwansa, Lauyansa Barr. A’isha Abdulkadir ta gabatar da shi a matsayin shaida shi kadai kuma ta roki a yi masa afuwa. 

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN