Hukumar yan sandan jihar Kebbi a ranar Talata, ta gabatar da Cakin kudi miliyan N60m ga iyalan yan sanda shida, waÉ—an da yan bindiga suka kashe a bakin aiki.
Yan sandan sun rasa rayukansu a wani gumurzu da yan bindiga yayin da suke aikin gadi a kamfanin GB Food Company da ke kauyen Gafara, karamar hukumar Ngaski jihar Kebbi, ranar 15 ga watan Maris.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Kakakin hukumar yan sanda jihar, SP Nafi’u Abubakar, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, ranar Talata.
Kakakin ya ce kwamishinan yan sanda, CP Musa Baba, ne ya gabatar da Cakin kudin ga iyalan mamatan a madadin kamfanin GB Food Company.
Ya ce:
"An damƙa Cakin naira miliyan N60m ga iyalan yan sandan da suka rasu kuma kowane gida ya samu Naira miliyan N10m."
"Halin dattakon da Kamfanin da ya nuna ba ya tsaya iya tallafawa iyalan mamatan yan sandan bane kaɗai, har da kara wa dakarun yan sanda da ke aiki kwarin guiwar su ƙara zage dantse wajen yaƙi da ta'addanci."
Kwamishinan yan sandan ya shawarci iyalan su bi hankali da tsantsaini wajen amfani da tallafin a ɓangaren bukatun su na kudi.