Mutane 5 sun mutu, sama da 30 sun jikkata, gidaje 100 sun ruguza sakamakon guguwar iska da ta yi barna a Damaturu.


Akalla mutane biyar ne suka mutu, wasu 36 suka jikkata, sannan sama da gidaje 100 suka ruguje bayan guguwan ruwan sama da iska ta yi barna a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe, Mohammed Goje, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu. 

Ya ce tawagar SEMA da suka yi bincike da ceto a ranar 9 ga watan Mayu sun amsa kiran gaggawa da ’yan samari nagari suka yi, tare da tallafa musu wajen kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe.

“Wasu mutane 41sun jikkata yayin da wurare da al'umma da lamarin ya shafa suka hada da (1. Waziri Ibrahim Extension, 2. Abbari Extension, 3. NayiNawa, 4. Pompomari, 5. Majalissar dokoki, titin Gujba da 6. Maisandari) an kwashe su kuma Abin takaici 5 sun mutu (maza 2, mace babba 1, mata 2),” in ji Goje. 

Ya kara da cewa "Dukkan wadanda abin ya shafa suna karbar magani kyauta kuma tuni an sallami 23."

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN