Yanzu yanzu: Buhari ya umarci kamfunan waya su hana kira fita daga layukan da basu da rijista, duba ka gani


Gwamnatin tarayya ta umurci kamfanonin sadarwa da su hana duk wani kiraye-kirayen waya fita daga lauyukan da ba a alakanta da NIN ba daga yau Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022.

Layukan da abun ya shafa sune wadanda ba a riga an yiwa rijita tare da hada su da lambar shaidar dan kasa ba wato NIN.

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista- Buhari ga kamfanonin sadarwa.

Ikechukwu Adinde, daraktan hulda da jama’a na NCC da Kayode Adegoke, shugaban sashen sadarwa na hukumar NIMC ne suka bayyana hakan a wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Litinin, rahoton The Cable.

“A tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya bayar da umurnin domin aiwatar da shi da kuma fara shirin a watan Disamban 2020, daga cikin manufofin gwamnatin na tsaro da zamantakewa. 

An sha tsawaita wa’adin da aka bayar na hada lambar NIN da layukan sim sau da dama domin baiwa yan Najeriya damar bin wannan doka cikin yanci. 

FG ta kuma yi la’akari da kiraye-kirayen da kungiyoyi da dama – kungiyar kamfanonin sadarwa masu lasisi ta Najeriya (ALTON), kungiyoyin jama’a, kungiyoyin kwararru da sauransu suka yi domin kara wa’adin a baya.

“Saboda haka, shugaban kasa ya amince da bukatun masu yawa don tsawaita wa’adin hada NIN da layukan sim.

 Sai dai a wannan gaba da ake ciki, gwamnati ta kaddara cewa aiwatar da manufar hada NIN da sim na iya ci gaba, saboda an riga an kammala komai domin tabbatar da ganin yan kasa da mazauna sun ba shirin hadin kai. 

Aiwatarwar yana da tasiri kan dabarun gwamnati musamman a bangarorin tsaro da zamantakewa da kuma tattalin arziki.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN