Jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kashe 'yan bindiga da ke amfani da shanu a matsayin garkuwa a jihar Neja


Bayan samun sahihan bayanan ‘yan ta’addan da ke tafiya daruruwa zuwa maboyarsu a Kusasau, rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike da Operation Gama Aiki ta aike da wasu jiragen yakin sojojin saman Najeriya domin su kakkabe ’yan ta’addan a wurin.

Legit.ng ta tattaro cewa da isowarsu, an ga wasu ‘yan ta’addan da ke kan babura suna tahowa zuwa layin kogi, inda suke amfani da shanu a matsayin garkuwa a maboyarsu.

Kamar yadda aka saba, martani daga majiyoyi na cikin gida da kuma sojojin Najeriya da aka girke a kewayen sun bayyana cewa an kashe 'yan ta'adda 47 ciki har da manyan shugabanni biyu. 

Karin bayani ya zo tare da nuna jin dadin yadda jirgin yaki ya yi luguden wuta inda aka bayyana cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hari a wasu kauyukan da ke kewayen yankin.

Sanarwar da Rundunar Sojin saman Najeriya ta fitar ta bayyana cewa, jami’anta za su kasance:

"Za mu ci gaba da gudanar da harin jiragen yaki a cikin jihar da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita don kawar da 'yan fashi a yankin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN