Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani Masallaci a Soyoye da ke karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun, sun yi garkuwa da wani sufeton ‘yan sanda da wasu mutane biyu masu ibada.
An yi garkuwa da dan sandan, Insifekta Kamarudeen Bello, wanda kuma shi ne Babban Limamin Masallacin kwanaki hudu bayan matarsa ta haihu.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalan wadanda lamarin ya shafa, inda suka bukaci a biya duk wanda aka kashe Naira miliyan biyar kudin fansa. Yanzu haka dai wadanda aka yi garkuwa da su sun samu ‘yanci bayan an biya su kudin fansa.
Majiyar ta shaida wa jaridar;
“An tuntubi matar Insifeto Kamarudeen da lambar wayar daya daga cikin wadanda aka sace.
“Ban san ko nawa kowannen su ya biya ba, amma ina ganin sufeton ‘yan sandan ya bayar da kusan Naira 700,000 kafin a sake shi.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sace mutanen tare da sako mutanen a ranar Lahadi. Oyeyemi, ya ce bai da masaniya ko an biya wani kudin fansa.