Honarabul Akogun Olùgbenga Omole, shugaban kwamitin labarai ne na majalisar Jihar Ondo, ya sha da kyar yayin da ‘yan bindiga suka kai masa farmaki a ranar 31 ga watan Maris. Legit ta ruwaito.
‘Yan bindiga sun kai wa Omole wanda dan majalisa ne karkashin jam’iyyar APC farmaki inda suka dinga harbin motarsa a ranar Alhamis da dare.
Wanda ya tabbatar wa TVC News, ya ce mummunan lamarin ya faru ne a Akure, babban birnin jihar.