Ko waye Abubakar Malami? duba takaitaccen tarihinsa da sirri daya da ya kamata ka sani


Abubakar Malami, Musulmi ne kuma Bafulatani. An haife shi ranar 17 ga watan Aprilu 1967 a garin Birnin kebbi, babban Birnin jihar Kebbi, a Arewacin Najeriya. Jaridar isyaku.com ya samo.

Ya fara karatunsa na Boko a makarantar framare na Nassarawa a garin Birnin kebbi, daga bisani ya tafi makarantar sakandare na College of art and Arabic studies. Ya sami Digirinsa na farko a Jami'ar  Usman Dan Fodio da ke Sokoto a 1991. Ya je makarantar koyon aikin Lauya a 1992.

Ya yi karatun Digiri na biyu a Jami'ar Maiduguri inda ya karanci Public administration a 1994. Bayan ya kammala Digiri na biyu, Malami ya kama aikin Lauya, har ya zama Lauyan Gwamnati, ya kuma rike mukamin Alkalancin Majistare a jihar Kebbi.

Malami ya zama mai ba da shawara kan harkokin shari'a na kasa a tsohuwar jam'iyar Congress for Progressive Change (CPC).

Yana cikin jiga-jigan Yan siyasa da suka kafa jam'iyar All Progressives Congress (APC) a  2013, kuma jagoran tsarin ganin sauran jam:iyyun siyasa kamar su  Congress for Progressive Change (CPC), Action Congress of Nigeria (ACN) da All Nigeria Peoples Party (ANPP) sun hade waje daya a 2014,

Abubakar Malami ya tsaya takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi, amma ya janye wa Abubakar Atiku Bagudu kuma ya mara masa baya a karkashin jam'iyar APC lamari da ya kai Atiku Bagudu zama Gwamnan jihar kebbi.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN