Wani jirgin kasa na daukar kaya da ya taso daga Lagos kan hanyarsa ta zuwa Kano ya zame daga hanyarsa a jihar Kaduna ya fadi kuma ya kashe direban jirgin.
shafin isyaku.com ya samo cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis a kauyen Farin Ruwa da ke kusa da garin Jaji a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.
Rahotanni na cewa jirgin ya dauko lemun kwalba ne daga Lagos zuwa Kano kafin faruwar lamarin da ya auku kwanaki kadan bayan yan bindiga sun kashe mutane da dama tare da sace wasu bayan sun dana wa hanyar jirgin kasa bam a karamar hukumar.