Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci sun kashe Hakimi ana tsakar yin Sallah


Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani masallaci a garin Maisamari a karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba, sun kashe wani Hakimi Alhaji Abdulkadir Maisamari. 

An kashe Maisamari ne a lokacin Sallar Isha’i a daren Litinin. Shaidun gani da ido sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun bude wuta ne nan take suka kutsa kai cikin Masallacin.

An ce mazauna garin sun yi tir da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani dutse da ke kusa da garin.

Wani mazaunin garin mai suna Musa Sale ya shaidawa manema labarai cewa babu wanda aka sace, kuma an binne Hakimin gundumar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Wannan shi ne Masallaci na uku da wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a jihar. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN