Rundunar ‘yan sanda ta fara gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin wata mata mai juna biyu da mijinta ya yi mata mai suna Taofeek Gbolagade.
Rahotanni sun bayyana cewa Taofeek ya ci zarafin matarsa a gidansu da ke Ogbere Housing Estate, Ibadan, da sanyin safiyar Talata 12 ga watan Afrilu.
Yayin da wasu ke cewa mutumin ya ci zarafin matarsa ne saboda rashin shirya Sahur (Abincin da Musulmi ke ci da Abuba lokacin Azumin watan Ramadan) a kan lokaci, wasu kuma na ganin ba wannan ne ya sa mutumin ya doke matarsa ba.
An ce mutumin ya sha dukan matarsa mai ciki sama da mintuna 30 kafin ta yi nasarar tserewa ta bar gidan.
Taofeek ya gudu ne bayan da ‘yan uwan matar suka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin.