Yadda wasu barayi suka sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya


Wasu gungun barayi sun tafka sata da tsakar rana inda suka yi awon gaba da gadar karfe mai tsayin mita 18.3 kan rafin Ara-Sone, garin Rohtas a gabashin kasar Indiya. 

Legit.ng ta labarta cewa Kakakin Hafsan yan sanda, Subhash Kumar, wanda ya tabbatar da hakan ga AFP ya bayyana cewa barajin sun yi basaja ne da kayan ma'aikatan gwamnati. 

Yace: 

Sun dauke gadar cikin wata babbar mota." 

A cewar yan garin Rohtas, barayin sun kwashe kwanaki uku suna kokarin sace gadar. 

Mazauna garin sunce sun yi mamakin yadda gadar tayi batar dabo duk da nauyinta ton 500.

An gina gadar ne a shekarar 1972 a garin Amiyawar. Bincike ya nuna cewa barayi sun dade suna kokarin sace gadar tun lokacin da aka gina wata sabuwa na siminta kusa da ita. 

Kakakin yan sandan, Kumar, ya ce tuni an sanar da masu siyan kayan karafuna su garzaya wajen hukuma idan suka ga wani da gadar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN