Sifeto Janar na yansanda IGP Alkali ya sake yin sintiri kan titin Abuja zuwa Kaduna


A ranar Asabar, Sifeto Janar na yan sandan Najeriya, IGP Usman AlkaliBaba, ya sake komawa sintiri babban titin Abuja-Kaduna domin duba jami'an tsaron da ya zuba don tabbatar da tsaro.

IGP Alkai ya tafi sintirin ne bayan halartan daurin auren diyyar Gwamnan jihar Delta a Cocin tarayya dake Abuja ranar Asabar, 9 ga Afrilu, 2022. Legit.ng ta ruwaito.

Ya umurci rundunar yan sandan sama sun zurfafa sintirin sama a hanyar da cikin garin Kaduna don taimakawa rundunar kasa don neman bayanan leken asiri.

Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakana jawabin da ya saki da yammacin nan.

A cewarsa, IGP ya jaddada niyyar tabbatar da isasshen tsaro a fadin tarayya don jin dadin al'umma.

Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

Makon da ya gabata mun kawo muku cewa Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Usman Alkali, ya jagoranci sintiri na musamman zuwan titin Abuja zuwa Kaduna ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, 2023.

IGP Alkali tare da dinbin jami'an yan sanda sun dira titin da tsagerun yan bindiga suka addaba don ganin abin da ke gudana.

Prince Olumuyiwa Adejobi yace IGP Alkali ya baza jami'an tsaro masu muggan makamai don tabbatar da tsaro titin.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN