Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin Duniya


Jagoran harkar tallafin majalisar dinkin duniya dake Najeriya, Legit.ng ta ruwaito Matthias Schmale, ya bayyana cewa ana bukatar $351m don taimakawa al'ummar yankin Arewa maso gabas 

Matthias Schmale ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a taron janyo hankali kan abinci da kiwon lafiya a birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable. 

Ya ce sama da yan Najeriya milyan 8.4 ke bukata tallafi a Najeriya, kuma babu kudi. A jawabinsa yace: "A fadin Arewa maso gabashin Najeriya, mutum milyan 8.4 na bukatan tallafi. Abin takaici, rabin wannan mutane - 4.1m - zasu shiga halin bakin yunwa bana." "Idan ba'ayi gaggawan samar da kudi ba, kimanin mutum milyan uku dake bukatan abinci na iya halaka." 

Rashin wannan taimako da bakin yunwa na iya jefa mutane karuwanci, amfani da kananan yara wajen ayyukan da sukafi karfinsu, da sayar da dukiyoyinsu." "Na samu labarin cewa a bara, mutane a Arewa maso gabas na cin ciyawa don kada su muu. Ina tsoron hakan ya maimaita kansa idan bamu dau matakin gaggawa ba." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN