
An tsinci gawar wani matashi da ba a san ko wanene ba, wanda aka jefar da shi a bayan gini a Jos (Hotuna)
April 13, 2022
Comment
An tsinci gawar wani matashi da har yanzu ba a tantance ba a jibge a bayan wani gini a garin Jos na jihar Filato.
An gano gawar ne a bayan Kings with Queens suites a unguwar Sabon Gari da ke Tudun Wada da safiyar Talata 12 ga watan Afrilu.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin mutuwarsa ba amma mutumin da alamun ya samu rauni a kansa.
'Yan sanda sun isa wurin da misalin karfe 8:00 na safe inda suka dauke gawar.
0 Response to "An tsinci gawar wani matashi da ba a san ko wanene ba, wanda aka jefar da shi a bayan gini a Jos (Hotuna)"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka