Watan Ramadan: 'Yan sandan sun hana yi 'Tashe' a Kano, sun bada dalili


Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta hana yin wasan ‘Tashe’, al’adar da aka saba yi duk shekara da watan Ramadan bayan kwanaki 10 na farkon watan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Legit ta wallafa cewa Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a ranar Litinin 11 ga watan Afirilu, inda ya ce akwai bata-garin da suke amfani da tashe suna tafka barna.

Akwai dalilai na matakin

Kamar yadda Kiyawa ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano tana farin cikin sanar da jama’a cewa ta dakatar wasan gargajiya (Tashe) wanda ake yi bayan ranakun farko 10 na watan Ramadan.

“Hakan ya biyo bayan ganin yadda wasu bata-gari suke amfani da damar wurin aiwatar da miyagun ayyuka kamar sara-suka, kwacen wayoyi da shaye-shaye.”

Ita ma Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ma ya yi kira ga mazauna jihar, muasamman iyaye da su ja kunnen yaransu daga keta dokoki.

Rundunar ta bayar da lambobin da za a tuntube ta idan wani abu ya taso

Takardar ta ci gaba da cewa:

“Duk wanda aka kama yana keta dokoki za a ladabtar da shi. Muna yi wa kowa fatan yin azumi lafiya.

“Idan akwai wani abu da ya taso na gaggawa, ana iya tuntubar rundunar ta wadannan lambobin, 08032419754, 08123821575, 08076091271. 09029292926 ko kuma a bi wannan adireshin na yanar gaizo, “NPF Rescue Me” wanda za a iya samu a manhajar Play Store. Mun gode kuma Ubangiji ya yi albarka.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN