Manajan Daraktan NRC, Engr. Fidet Okhiria, ranar Litinin ya bayyana cewa lambobin waya 51 a cikin takardar an kashe ko dai ba a iya samun su tun safiyar Talata.
Ya kara da cewa lambobin waya 35 da ke cikin takardar sun yi kara amma babu amsa daga daya bangaren yayin da lambobin waya 60 da aka kira ba a dauka ba.
Da yake bayyana cewa adadin wadanda aka tabbatar sun mutu ya rage saura takwas, ya kuma yabawa hukumomin tsaro da duk goyon bayan da suka bayar.
"Muna matukar godiya da ziyarar da Kwamandan Squadron MOPOL 1 Kaduna ya kai a inda hatsarin ya faru a yau (jiya)," in ji shi.
Dangane da kokarin dawo da hidimar, NRC MD ta ce kociyoyin biyu (SP 00016 da SP 00017) da aka sake dawo da su tun da farko an koma da su tasha ta Rigasa cikin koshin lafiya wanda ya kawo adadin kociyoyin da aka kwato kuma suka koma tashoshin NRC zuwa bakwai.