Wani mutum mai suna Mohammed Sani ya rasu yayin da yake tsakar jagorantar Sallar Tuhajjud da misalin karfe 4 na Asuba.
Lamarin ya faru ne a yankin Samari da ke Birnin Zaria a jihar Kaduna ranar 24 ga watan Afrilu dai dai da 23 ga watan Ramadan.
Babu wani cikakken bayani kan musabbabin rasuwarsa kawo yanzu. Sai dai mun samo cewa za a yi jana'izarsa da karfe 8:30 na safiyar Lahadi 24 ga watan Afrilu.