Yan bindiga sun raba kayan fitar Salla ga jama'a, sun sace wata Mata da diyarta bayan rabon kayakin a jihar Kaduna


Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna legit ta labarta
.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.

Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama'a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai da labarin faruwar lamarin.

Ya ce:

“Kun san mutane basa kaiwa yan sanda rahoton irin wannan lamari a nan take.”

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN