Wata majiya mai tushe da ke kusa da Minista ta tabbatar cewa Ministan shari'a kuma Antoni janar na Najeriya Abubakar Malami SAN, bai taba sa wani ya ci zarafin wani dan siyasa ba a tarihin rayuwarsa kazalika ya bar duk masu cin mutuncinsa tare da yi masa kazafi da Allah.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo wannan sirri ranar Asabar 2 ga watan Aprilu wanda ya zo daidai da daya ga watan Ramadan 1443AH.
Biyo bayan maganganu da suka dinga yawo a wani gidan Radiyon FM da kuma wasu yara da ke ta rubuce rubucen batanci, lamari da ke kara durkusar da martabar jihar Kebbi a ajin jihohin Arewacin Najeriya bisa manufa ta wayewa da juriyar zamantakewa.
Kazalika, isyaku.com ya samo cewa Malami baya da masaniya kan lamarin cacan baki da ke gudana a fagen siyasar gidan rediyon FM ko ire-iren rubuce-rubucen batanci da ake zargin wasu mutane na yi a jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce tun farko Malami bai umarci kowa ya yi irin wannan cacan baki da sunansa, saninsa, ko izininsa ba.
Mun samo cewa hidimar yi wa jama'a aiki tukuru a mataki na kasa, da kuma kasa da kasa, duba da irin kaluble da ke ofishin Ministan shari'a shi ke gaban Abubakar Malami ba fada da yan'uwa yan gida jihar Kebbi ba kawai don sha'anin siyasa.