Kwamitin Masallacin Apo ya dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci


Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen Æ´an majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid kan hudubarsa ta ranar Juma'a.

BBC ta ruwaito cewa Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma'a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.

"Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe," in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa.

A cikin wani saƙo da shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya aika wa BBC, ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama'a.

Sanarwar ta ce: "Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin Æ´an Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci."

"An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma'a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai 'yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi."

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

Sanarwar ta ƙara da cewa "ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da waɗanda suka saɓa wa Allah, da masu zaɓe da kuma ƙasa."

Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta saɓa wa addinin Islama. Kuma a cikin sanarwar kwamitin ya naɗa sabbin lamamai na Masallacin inda Malam Mohammad zai yi tafsiri, yayin da kuma Malam Abdullahi zai jagoranci Juma'a.

Babu wani martani daga Sheikh Nuru Khalid game da matakin da kwamitin ya ɗauka na dakatar da shi, kuma BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar malamin amma wayarsa a kashe.

Sheikh Nuru Khalid ya sha caccakar gwamnati kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, kuma hudubarsa na zuwa ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa a ranar Litinin inda har yanzu ba a san adadin mutanen da suka kashe ba da waɗanda suka sace.

A cikin huɗubar Malamin ya ambaci wani da ke cewa "harakar tsaro ta zama kasuwanci a Najeriya, jinin talaka ya zama kayan kamfen a kasar nan, sai zaɓe ya kusa kashe kashe zai karu."

"Mun dade muna hakuri - hanya ba kyau, talauci mun hakura, tsadar rayuwa mun hakura, karya mun hakura, kwashe kudin kasa mun hakura, ku bar mu mu zauna da ranmu kuma ba zai yiyu ba?"

Don haka a cewar Malamin abin da ya kamata talakan Najeriya ya yi shi ne ya ƙauracewa zaɓe har sai an daina kashe rayukan al'umma.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN