Abin da Malamin makarantar Allo ya yi wa Almajiri dan shekara 8 zai ba ka ..


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani malamin makarantar Allo mai suna Ma’aruf Muhammad, mai shekaru 24, bisa zargin gallazawa wani yaro Almajiri mai shekaru 8 mai suna Muhammad Garba. Shafin Jaridar isyaku.com ya labarta.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kama kakar da mahaifin yaron.

Jami’in PPRO ya ce an kai rahoton faruwar lamarin ga hukumar ne bayan da aka gano yaron yana yawo a wani rami da ke kusa da Kofar Mata Quarters a birnin Kano. 

“A ranar 29/03/2022 da misalin karfe 1400 na safe, an samu rahoto daga manajan darakta na hukumar kwashe mabarata ta jihar Kano cewa a ranar 28/03/2022 wani Malam Usaini Uba, ‘m’, na jihar Kano. Kofar Na’isa Quarters, Kano ta kawo wa hukumar, wani Muhammad Garba ‘m’ dan shekara 8, "Almajiri”, wanda aka same shi yana yawo a cikin wani rami, kusa da kofar Mata Quarters a birnin Kano, da tabo a ko’ina a jikinsa sakamakon azabtarwa da ake zarginsa an yi ma shi," in ji Kiyawa. 

“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya taso tare da umurci tawagar ‘yan sanda a karkashin SP Umar Sa’id Abdullahi da su gudanar da bincike mai zurfi. Nan take aka dauki matakin, inda aka garzaya da yaron zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, inda aka yi masa magani aka sallame shi.

“A binciken farko da aka yi, Almajirin ya bayyana cewa shi dan asalin garin Nguru ne na jihar Yobe, kuma ya tsere zuwa jihar Kano ta jirgin kasa sakamakon mummunan duka da malaminsa da ke makarantar “Almajiri” wani Ma’aruf Muhammad ya ci gaba da yi masa. Tsawaita bin diddigin lamarin ya kai ga kama malamin makarantar “Almajiri”, Ma’aruf Muhammad, ‘m’ mai shekaru 24 a unguwar Garbi Quarters, karamar hukumar Nguru, jihar Yobe a wata maboya a karamar hukumar Toro, jihar Bauchi.

“A bisa bincike na gaskiya, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya kuma kara da cewa ya yi amfani da wayar USB Cable wajen lakadawa wanda Almajirin duka a lokuta da dama bayan ya cire rigarsa, kakar yaron mai suna Talle Muhammad 'f'  Yar shekara 65 a Duniya ce ta kawo masa yaron. Daga baya aka kama ta, kuma an kama mahaifin yaron. 

Kakakin ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN