Sakamakon bincike ya yi wa Malami walle kan cewa Buhari bai sake dinki ba tun hawansa mulki


Sakamakon wani bincike da shafin labarai na isyaku.com ya yi, ya nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi dinke-dinken tufafi kamar kowa tun hawansa mulki zuwa yanzu.

Biyo bayan ce-ce-ku-ce da ya samo asali sakamakon yadda wani Malami ya dinga yayata cewa saboda tsananin tattali shugaba Buhari bai ko dinka sabon tufafi ba. Lamari da ya haifar da muhawwarar ba gaira ba dalili a shafukan sada zumunta har wasu na amfani da wannan damar domin taba martabar shugaba buhari a soshiyal midiya.

Binciken dai ya samo tabbacin cewa shugaban ya yi dinke-dinke domin ba shi damar daidaita da zamani domin kuma samun sukunin shiga jama'a a matsayinsa na shugaban kasar Afrika da ta fi kowace kasar bakar fata yawan jama'a a fadin Duniya.

Ku biyo mu domin samun cikakken rahotun sakamakon binciken....

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN