Iyayen dalibai sun yi wa maigadi dukar tsiya domin ya hanasu shiga makaranta saboda rashin yin allurar cutar covid


Wasu iyaye su uku sun yi wa wata mai gadin makaranta dukar tsiya a Brooklyn, New York City saboda ta hana su shuga makarantar domin badu da takardar shaidar cewa sun yi allurar rigakafin cutar COVID lamari da ya sa aka kwantar da ita a asibiti. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Ranar 7 ga watan Aprilu iyayen da suka hada da maza guda biyu da Mata guda sun ziyarci makarantar domin su gan yayansu. Daya daga cikin yaran da iyayensa suka zoyarta zai yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ne watau birth day kuma mahaifinsa ya zo masa da kyautar Pizza da sauran kyautuka.

Sai dai rigima ya kaure a bakin kofar shiga makarantar domin mai gadi ta hana iyayen shiga makarantar sakamakon rashin takardun shaidar allurar COVID.9

Kakakin  yansandan BrooklynBrooklyn, Gregory Floyd, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 2 na rana kuma yansanda na bincike kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN