Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar masu neman kafa Biafara, IPOB, sun kai wa motar sintiri na sojoji hari a Aba, a Jihar Abia. Rahotun Legit.ng.
The Nation ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Juma'a a lokacin da sojojin ke aikin sintiri.
An gano cewa maharan sun labe ne sun kai wa sojojin harin kwantar bauna.
Lamarin ya faru ne a shahararren mahadar Tonimas da ke karamar hukumar Osisioma a babban hanyar Enugu-Aba-Port Harcourt, rahoton The Nation.
Maharan sun kuma kona motar sintirin sojojin.
Amma, a yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba sakamakon harin.
Wata majiya daga hukumomin tsaro ta ce lamarin ya faru ne misalin karfe 3 dare.
An tattaro bayanai cewa lamarin ya janyo tashin hankali a unguwar inda mazauna ke zaman dar-dar.