Wani dan Najeriya mai suna Azeez ya bude wajen dafa abincin shinkafar jellof da aka fi sani da Mama put kiri kiri a filin Allah a birnin London, lamarin da ya sanya turawa shiga layi domin siyan abincin.
A cikin wani hoto da @IamOlajideAwe ya wallafa a shafin Twitter , an iya ganin wasu mutanen Oyinbo yayin da suke layi don siyan abinci a gidan abincin.
Azeez yace:
"Ni dan Legas ne Surulere, muna zaune a Landan don haka muka yanke shawarar kawo abinci a cikin birni, muna biyu lokacin da muka fara amma yanzu, ni kaina nake yi."
Lokacin da @IamOlajideAwe ya raba tweet, ya haifar da sha'awa daga 'yan Najeriya wadanda suka yaba da ruhin mutumin.