Mataimakin gwamnan Sokoto, SSG, shugaban ma'aikata, kwamishinoni 11 sun yi murabus


Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya amince da murabus din mataimakinsa, Alhaji Manir Dan’iya, sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Sa’idu Umar da wasu masu rike da manyan mukaman siyasa 11 a jihar.

Wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya fitar a Sokoto ta bayyana hakan a ranar Laraba 27 ga watan Afrilu.

Sanarwar ta ce;

“Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya amince da murabus din wasu masu rike da manyan mukamai goma sha uku a gwamnatin sa, wadanda suka hada da Hon. Manir Muhammad Dan Iya, mataimakin Gwamnan jihar wanda kuma shine mai kula da ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu.

Ragowar kwamishinonin dai sun hada da ma’aikatun kudi, muhalli, matasa da wasanni, filaye da gidaje; da Sana'o'i da Tsaro: Hon. Abdussamad Dasuki, Hon. Sagir Bafarawa, Hon. Bashir Gorau, Hon. Aminu Bala Bodinga da Col. Garba Moyi (rtd) bi da bi.

Sauran kwamishinonin da suka yi murabus din sun hada da na kasuwanci, ayyuka, albarkatun ruwa, daskararrun ma’adanai da harkokin addini: Hon. Bashir Gidado, Hon. Salihu Maidaji, Hon. Shuaibu Gwanda Gobir, Hon. Abubakar Maikudi Ahmad da Hon. Abdullahi Maigwandu.

Daga cikin wadanda suka yi murabus sun hada da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Sa’idu Umar da shugaban ma’aikata, Mukhtar Umar Magori.” Inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN