
Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano
April 28, 2022
Comment
Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano (PCACC) ya bayyana cewa Janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya), Diraktan hukumar kare hakkin masu siyayya, ya gudu daga hannunta. Legit.ng ta ruwaito.
Mukaddasin shugaban hukumar PCACC, Barista Mahmoud Balarabe, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba.
A bisa rahoton Daily Trust, Balarabe ya ce suna cikin yiwa Dambazau tambayoyi a hedkwatar hukumar ranar Talata sai ya bukaci zuwa gida shan magani.
Balarabe yace an jami'an hukumar suka raka shi gida amma kafin su ankara yayi layar zana.
Ya ce tuni suna gayyatar Dambazau amma ya ki zuwa sai ranar Talata bayan sun yi barazanar damkeshi.
Balarabe ya kara da cewa sun gayyacesa ne bisa zargin rashawa da ake masa.
0 Response to "Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka