SOJA YACI AMANAR TSARON NIGERIA YA KASHE KANSA
Wannan sojan da kuke gani a tube an saka masa ankwa, sunansa Jibrin Umar, yana da mukamin Lance Corporal a gidan sojin Nigeria, asalinsa dan garin Biu ne a jihar Borno. Arewa intelligence ta ruwaito.
Lance CPL Jibrin Instructor ne na sojoji da yake aiki tare da bataliyar sojoji dake garin Geidam a jihar Yobe, sati biyu da suka wuce ya bata ba'a ganshi ba
Ranar Lahadi da ta gabata, Boko Haram ISWAP sun kaddamar da harin ta'addanci a garin Geidam kuma an ganshi a cikin tawagar 'yan Boko Haram din da suka kawo hari, Commanding Officer na Sojoji yayi tracking nambar wayansa aka ganoshi a wani gurin da 'yan Boko Haram su ke mai nisan kilomita sama da 200 daga inda yake aiki a garin Geidam
An tura da sako zuwa sansanin Sojoji dake fadin jihar Yobe akan a saka ido domin a kama Lance Cpl Jibrin idan an ganshi tunda an tabbatar yana cikin tawagar 'yan Boko Haram
Shekaran jiya Talata, Jibrin yayi shigar bultu domin ya badda kama, ya baro cikin 'yan Boko Haram ya shigo gari yazo ya hau mota a Gashua zai tafi garin Gombe, Allah Ya bada sa'a sojoji da suke aiki a Checking point suka ganoshi suka kamashi
Sojojin sun dauki Jibrin a mota daga inda suka kamashi zasu kaishi sansanin sojoji dake Geidam domin ya fuskanci hukunci, shine sai ya kwace bindiga daga hannun wani soja da suke rakashi ya bindige kansa har lahira
Kafin Sojan ya bindige kansa, lokacin da sojoji suka kamashi a Checking point da suke tambayarsa ya tabbatar da cewa shi Dan Boko Haram ne, yana musu aikin leken asiri da horar dasu dabarun yaki, kuma yace suna da yawa, har ma ya fadi sunayen wasu sojoji da suke yiwa Boko Haram aiki, an kama wasu daga cikinsu
Amma bayanan sirrin sojoji da aka tatsa daga bakin Lance CPL Jibrin kafin ya harbe kansa sun tabbatar da cewa akwai sojoji 'yan Boko Haram masu yawa da suke cikin bataliyar sojoji na Geidam da kuma Gombe, suna nan sun boye kansu suna yiwa Boko Haram aiki a halin da ake ciki.