Manyan mutane da masu fada aji a Zamfara ne ke da hannu wajen ta’addanci da kashe-kashe – Gwamna Matawalle


Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi zargin cewa wasu manyan mitane da masu fada aji suna daukar nauyin 'yan ta'adda a jihar.

Jihar Zamfara dai ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

A ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, ‘yan bindiga sun sace wasu dalibai mata 5 na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe a Jihar Zamfara.

Da yake mayar da martani, gwamnan jihar, Matawalle ya ce wasu manyan mutane ne ke daukar nauyin 'yan bindigar.

Ya kuma yi zargin cewa ‘yan bindiga sun dauki mazauna jihar aiki a matsayin masu ba su Labaran sirri.

Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai Zailani Bappa, ya ruwaito gwamnan yana fadar haka a cikin wata sanarwa da ya fitar: “Karfafan bayanai na nuni da cewa yawaitar ‘yan fashi da makami a jihar galibi ‘yan asalin jihar ne ke taimakawa masu yin danyen aikin..

"Har ila yau, akwai, a cikin jama'ar da ke karbar 'yan tsirarun kudade don yi wa 'yan fashi aikin ba da labarin sirri."

Matawalle ya ce a bisa dalilin da ya sa aka umarci masu rike da mukaman siyasa a jihar da su rantse da Alkur’ani yayin da suke rantsuwar kama aiki.

Sai dai ya ce wasu manyan ‘yan siyasa a jihar sun ki yin amfani da kur’ani wajen rantsuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN