Malaman addini 6 sun rasu a hadarin mota a hanyarsu ta dawowa daga da'awa a Kano


Malaman addinin Musulunci masu wa'azi guda shida sun rasa rayukansu a jihar Kano ranar Laraba sakamakon mumunan hadarin mota yayin dawowa daga wajen da'awa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Malaman sun yi hadarin mota ne na hanyar komawarsu gida daga karamar hukumar Sumaila. Rahotun legit.

Wata jami'in gidauniyar Imam Malik da suka dauki nauyin da'awar ta bayyana cewa sun samu labarin hadarin ne misalin karfe 3 na rana.

A cewarta, labarin da suka samu shine dukkan Malamai shida dake cikin tawagar da'awar sun rigamu gidan gaskiya.

Ta ce har yanzu ba'a samu bayanai kan sauran wadanda suka raka malaman ba.

Tace:

"Mun taru yanzu a gidauniyar dake unguwar Dakata. Zamu je gidan Sheikh Alkassim Zakariyya don jana'izarsu."

Wasu daga cikin dalibansu sun yi jimamin rashin malaman a shafin ra'ayi da sada zumuntar Facebook.

An tattaro cewa daga cikin wadanda suka rasu akwai Sheikh Alkassim, Isiya Tela, Malam Ishaq Rummawa, da Mustapha Musa Sa’ad.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN