Wani mummunan lamari ya afku a cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ta Oredo da ke karamar hukumar Oredo ta jihar Edo, yayin da wani mutum da ba a tantance ko wanene ba ya mutu bayan ya fada cikin wata Ramin aje ruwan Masai watau soakaway.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan da matashin mai matsakaicin shekaru ya bar dogon layi da yake ciki don yin rajistar yin aikin jinya kyauta don yin fitsari.
Shedun gani da ido sun ce cikin kuskure ya taka wata margin soakaway da ke cikin harabar gidan . Aminiya ta ruwaito cewa, babu wata alamar taka-tsantsan da aka rubuta ko aka saka, sai mutumin ta taka mrgin kum nn take ya tsunduma cikin rmin ruwan masai.
Wannan lamari ya haifar da rudani tsakanin jama'a da ke wajen . An dauki awanni hudu kafin a iya fito da mutumin da ya fada cikin ramin Masai tare da taimakon wata na'ura.