Kebbi: Yadda aka yi wa matar aure da diyarta kisar gilla a cikin gidanta a garin Birnin kebbi, cikakken rahotu

Dakin da aka kashe Sadiya da diyarta Khadijat

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta tabbatar da kisan wata matar aure mai suna Sadiya Idris yar shekara 23 tare da diyarta mai suna Khadijat mai shekara 4 da haihuwa bayan an yi masu kisar gilla cikin daren ranar Lahadi 10 ga watan Aprilu 2022 a Unguwar Kamfanin cashe shinkafa na Labana Rice Mills da ke byepass Birnin kebbi. Shafin Jaridar isyaku.com ya ruwaito.

Mun samo cewa wacce aka kashe matar wani fitaccen mai sana'ar Tela ne mai suna Akilu Altine. An kashe matar da diyarta mai shekara 4 da haihuwa amma aka bar jaririya mai wata 3 da haihuwa wacce matar ke shayarwa

An sare matar da diyarta a wurare da dama

A wani yanayi na rashin Imani, maharan sun sassare sassan jikin matar a wurare da dama, kazalika sun sassare diyarta yar shekara 4 da haihuwa.

Sai dai shafin isyaku.com ya lura cewa ana zargin cewa maharan basu dauki komi a dakin ba, domin hatta wayar salularta ba a dauka ba bayan an kasheta. Lamari da ke haifar da zargin cewa kila maharan sun je ne kawai domin su halaka matar.

Kazalika mun lura cewa maharan basu yi amfani da katfi wajen balle kofar shiga dakin ba, kuma sun sami mariganyar ne kwance a kan katifar gadonta kuma a cikin dakinta kamar yadda alamu suka nuna bayan an gan gawarta da safe ranar Litinin.

Yadda lamarin ya faru

A kan wannan katifa aka kashe Sadiya

Shafin isyaku.com ya samo cewa tunda lokacin watan Ramadan ne, mijin matar Malam Akilu yakan kwana a shogo ne domin cika alkawarin dinkin jama'a. Kuma yakan dawo gida da karfe 4 na asuba domin yin. Sahur. Kuma yakan jira har sai ya yi Sallar Asuba kafin ya koma shago.

Sai dai ranar Litinin 11 ga watan Aprilu, Akilu ya dawo gida sai ya tarar da abin da ya faru da iyalinsa. Wata majiya ta tabbata mana cewa Akilu ya suma saboda tsananin kaduwa da lamarin kuma aka garzaya zuwa Asibiti da shi domin samun kulawar gaggawa.

Yansanda sun fara bincike 

Shafin isyaku.com ya samo cewa Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Kwamishinan yansandan jihar Kebbi CP Musa Baba ya umarci jami'ansa na sashen ofishin yansanda na garin Birnin kebbi, da na sashen binciken manyan laifuka da leken asiri CIID, su kaddamar da bincike a kan lamarin tare da gano wadanda suka aikata wannan laifin domin hukunta su.

Al'umman garin Birnin kebbi sun sa ido domin jin sakamakon binciken yansanda kan wannan lamari da ya shiga jerin irin kashe-kashen jama'a da ya gudana a cikin garin Birnin kebbi daga 2015 zuwa yau. 

Khadijat yar shekara 4 da aka kashe tare da mahaifiyarta Sadi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN