Kakakin hukumar yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya bayyana yadda ta faru bayan sun kama Idris Suleiman wanda ya kashe matar aure tare da diyarta a garin Birnin kebbi.
Ya ce wanda ya aikata laifin ya gaya wa yan sanda lokacin bincike cewa sun sami sabani da matar kuma ta kira shi dabba kuma wulakantaccen maigadi shi ya sa ya kutsa gidanta ya kasheta. Ya ce ya kashe diyarta ne saboda ta gane shi.
SP Nafi'u ya yi karin bayani kan lamarin.
Latsa kasa ka kalla
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221347534172950&id=1086336452