Da duminsa: An kama wanda ya kashe matar aure tare da diyarta a garin Birnin kebbi (Hotuna da Bidiyo)


Rundunar yansandan jihar Kebbi ta kama wani dan asalin garin Maradi a jamhuriyar Niger mai suna Idris Suleiman wanda ya yi wa wata matar aure Sadiya Idris tare da diyarta kisar gilla a Unguwar gidajen bayan Kamfanin Labana da ke garin Birnin kebbi. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

Rundunar ta ce ranar 11 ga watan Aprilu 2022 Idris ya ketara gidan wani Tela mai Suna Akilu Altine ya yi amfani da adda ya sare matarsa bayan ya kutsa kai zuwa cikin gida Akilu ya sami matarsa domin ramuwar fansar zagi da ya ce ta yi masa na kiransa Mai gadin banza a cewarsa bayan sun sami yar cacar Baki Yan kwanaki da suka gabata a lokacin.

Ya ce wannan ne dalili da ya sa ya shiga gidan ya kashe ta kuma ya buga kan diyar a tiles na tsakar dakin ne saboda ta kira sunansa, kenan ta game shi. Domin gudun kada ta tona masa asiri shi ne ya sa ya kashe diyar mai shekara 4 da haihuwa.

Wani abin mamaki shi ne, tare da shi Idris aka yi Sallar Jana'izar Sadiya, kuma shi ne ya rike kafafun diyarta bayan ya kashe su aka saka ta a cikin Kabari, kuma an yi zaman amsar gaisuwa tare da shi har kwana uku.

Latsa kasa ka kalli bidiyon jawabin dalili da ya sa ya kashe matar

https://www.facebook.com/134576693722549/posts/1385942885252584/


 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN