Fusatattun makwabta sun yi wa barawo duka har lahira a gaban mahaifiyarsa


Wani mummunan lamari ya faru a Takoradi, babban birnin yankin yammacin kasar Ghana, yayin da aka yi wa wani barawo duka har aka kashe shi a gaban mahaifiyarsa.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa, wani barawo, Nana Kwadwo Duah, ya sha dukan tsiya daga makwabtansu a garin Fijai saboda sata.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa barawon mai shekaru 30 ya dade yana tsoratar da mazauna garin Fijai da harkokinsa na sata.

Jama'a sun kama shi yana sata da misalin karfe 3 na safiyar Laraba 6 ga Afrilu, kuma suka yanke shawarar kawo karshen sa.

An tattaro cewa hawayen mahaifiyarsa da rokon da ta yi ta yi wa jama'a da ke dukansa bai wadatu ba har suka kashe shi. 

Mahaifiyar sa ta bayyana cewa dan nata yana sata ne domin ya biya bashin talabijin da ya sace daga wani makwabcinsu.

Kalli bidiyon a kasa..

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN