Da Ɗuminsa: Babban Kwamandan Boko Haram, Ibn Kathir, Ya Miƙa Wuya Ga SojojiHedkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce babban kwamandan kungiyar Boko Haram, Saleh Mustapha ya mika kansa ga dakarun Operation Hadin Kai, da ke arewa maso gabas. Legit.ng ta ruwaito.

Kawo yanzu yan ta'adda guda 51,114 ne suka mika wuya kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Direktan Watsa Labarai na Sojoji, Bernard Onyeuko, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan dakarun sojojin tsakanin 25 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu a ranar Alhami a Abuja.

Mr Onyeuko ya ce mika wuyan da Mustapha wanda aka fi sani da Ibn Kathir, wanda na hannun daman Qaid na Garin Ba-Abba ne, babban nasara ne ga sojojin da ke Bama, rahoton Daily Nigerian.

Ya kara da cewa kawo yanzu yan ta'adda 51,114 ne suka mika wuya, cikinsu akwai maza 11,398 da mata 15,381 sai yara 24,335 zuwa ranar 5 ga watan Afrilu.

A cewarsa tuni an dauki sunayen wadanda suka mika wuyan an adana, sannan farare hula da aka ceto an mika su ga hukumomin da ya dace kafin hada su da iyalansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN