Falasdinawa sun lalata Kabarin Annabi Yusuf a Nablus —Isra’ila


Mahukuntan Isra’ila sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke kara kamari tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra’ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. Aminiya ta ruwaito.

Wani shafin Twitter na gwamnatin Isra’ila ya wallafa wani bidiyo da ya ce ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya kunshi kabarin Annabi Yusuf.

Zuwa yanzu babu wani martani daga bangarorin Falasdinawan kamar yadda BBC ya ruwaito.

Yahudawa na girmama wurin da kabarin yake, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

An sha yin arangama a wurin, har ta kai aka kona kafin aka sake gyarawa.

Ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz ya bayyana al’amarin a matsayin “babban laifin saba ’yancin ibadah”.

Yankin Yamma da Kogin Jordan na fuskantar barazanar tsaro tun bayan farmakin da sojojin Isra’ila suka kaddamar bayan harin da aka kai a Tel Aviv da kuma cikin yankin Isra’ila.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN