An yi wa kasurgumin dan fashi da makami kamun kazan Kuku, duba yadda ta faru


Wani da ake zargin dan fashi da makami ne mai suna Isikilu Moses a safiyar ranar Juma’a, 8 ga watan Afrilu, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama shi a yayin da suke gudanar da wani samame na fashi da makami a unguwar Joju da ke Sango ota.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa an kama wanda ake zargin ne biyo bayan kiran da jami’an ‘yan sanda suka samu a hedikwatar sashin Sango, cewa ‘yan fashi da makami sun kai farmaki kan titin Adebeshi, daura da titin Joju, Sango ota, tare da kwace wa al’ummar yankin kayayyakinsu da karfin bindiga.

Da jin wannan kiran na bakin ciki, DPO mai kula da Sango, SP Saleh Dahiru, ya yi gaggawar tara tawagar sa da ke sintiri, suka nufi wurin da lamarin ya faru

Da ganin ’yan sandan ne, ‘yan ta’addan suka ranta na kare, amma sai suka dafa masu da gudu har suka kama daya daga cikinsu mai suna Isikilu Moses.

Ababen da aka damu a wajen shi sune; bindiga guda daya na kirar gida da wayoyin hannu guda biyu mallakar wadanda suka yi wa sata.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga hukumar binciken manyan laifuka da leken asiri ta jihar domin gudanar da bincike mai zurfi. Haka kuma ya bayar da umarnin gudanar da gagarumin farautar sauran ‘yan kungiyar da suka tsere da nufin gurfanar da su a gaban kuliya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN