Duba mutumin da ya fi kowa gajerta da ya yi zamani da Sarakunan Yarbawa guda uku


Ana kiran wannan mutum Baba Kekere, wanda ya fi kowane mutum gajerta a Fadar basaraken gargajiya na Alafin na Oyo. An yi imanin cewa ya zarce shekara 100 a Duniya
. Shafin isyaku.com ya samo.

Bayanai sun nuna cewa shi dan aike ne a Fadar Sarki. Ya kuma yi zamani da Sarakuna uku a Masarautar. Ya yi aiki da Sarakuna da suka hada da:

1. Oba Adeniran Adeyemi II, mahaifin Oba Lamidi daga 1945 zuwa 1956.

2. Oba Gbadegesin Ladigbolu II tsakanin 1956 zuwa 1968, da kuma

3. Oba Lamidi Adeyemi III, tsakanin 1970 zuwa 2022.

Ana kiransa Baba kekere ne saboda gajertarsa. Amma dai haziki ne mai aiki tukuru a cewar majiyarmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN