An kama matsafa biyu dauke da kan wani yaro bayan an kashe shi, duba abin da ya faru


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin aikata tsafi da sabon kai da hannayen wani yaro. 

Wadanda ake zargin, Wasiu Omonose da Akanbi Ibrahim, an kama su ne a hanyar Oke Oyi/Jebba, wajen babban birnin Ilorin da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce wadanda ake zargin da ke kan babur sun yi kokarin kaucewa kamasu da suka ga ‘yan sanda suna binciken ababen hawa. Sai suka juya suka nemin tserewa. Hakan ya sa jami'an tsaro suka bi su tare da tilasta musu tsayawa.

Okasanmi ya ce an gano wata jaka dauke da sabon kai da hannaye a hannunsu lokacin da aka bincike su. 

“A ci gaba da namijin kokarin da rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ke yi na ganin ta kawar da miyagun laifuka da duk wani nau’in aikata laifuka a jihar Kwara, jami’an ‘yan sandan da ke aiki da rundunar ‘Operation Harmony’ sun sanya ido kan mikiya, yayin da suke sintiri a hanyar Oke Oyi/Jebba a yau 24/4/2022 da misalin karfe 1130. Sanarwar ta kara da cewa, sun kama wasu mutane biyu ne a kan babur, inda suka yi yunkurin kaucewa jami’an da ke bincike, lamarin da ya sa jami’an suka fara zargin mutanen.

Ana cikin bincikensu ne sai aka gano wata jaka dauke da sabon kai da hannayen Dan Adam a hannunsu.

“Da ake yi masa tambayoyi, wadanda ake zargin masu suna Wasiu Omonose mai shekaru 35, a gidan Abioye, tare da wani Akanbi Ibrahim mai shekaru 32 a unguwar Sayo Street, sun bayyana cewa sun samo sabon kan ne da hannu daga wani Alfa a Ilorin domin yin tsafi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN