Ko an kashe basaraken Yarbawa Alafin na Oyo ne? Gwamnan PDP ya magantu


Gwamna Seyi Makinde na Oyo ya mayar da martani kan ikirarin cewa shi ne ke da alhakin mutuwar manyan sarakuna a jiharsa, ciki har da na Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi. 

Legit ta labarta cewa bayan rasuwar babban basaraken a ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, an yi ta rade-radin cewa tun da sarakunan Oyo ba su gaza uku suka rasu a gwamnatin Makinde ba, akwai yiwuwar yana da hannu a mutuwar Oba Adeyemi. 

Da yake magana a ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu, matashin gwamnan jihar, ya lura cewa ikirarin karya ba ne kawai, amma ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an yi jana’izar marigayin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito. 

Ko da yake ya bayyana cewa duk sarakunan da suka mutu kwanan nan a Oyo sun kai shekarun da suka wuce kafin su shiga kakanninsu, Makinde ya bayyana cewa komai ya kai shekarunsa babu wanda ya yi fatan mutuwar Oba Adeyemi. 

Kalamansa: 

“Komai shekarun Alaafin, da ba mu so ya shiga kakanninsa ba. Sa’ad da ya hau gadon sarautar kakanninsa, ina Æ™arami sosai. Amma saboda yadda Kabiyesi ya kasance a gare mu, da mun so mu kasance tare da shi har abada idan ya yiwu.

 “Don haka, mun yi bakin ciki amma kuma muna farin ciki domin Kabiyesi ya dade a kan karagar kakanninsa. 

“Na biyu kuma, tun da muka samu labarin mutuwarsa, a tsawon jiya, na samu kira daga fadar shugaban kasa da kuma abokan aikina da dama. Sarkin Musulmi da Sarkin Kano sun kira ni da kaina.”

 Haka kuma, a ziyarar aikin da ya kai masa na jajanta wa iyalan gidan marigayin, Gwamna Makinde ya shawarci Oyomesi da ke da alhakin zabar da kuma nada Alaafin na gaba da kada su bari tazarar ta kai ga gaci. 

Da yake magana game da ziyarar a shafinsa na Facebook, Makinde ya ce:

 “Da yammacin yau mun ziyarci fadar mahaifinmu, Mai Martaba Alaiyeluwa Làmídi Oláyíwolá Àtàndá Adéyemí III, Alaafin na Oyo, wanda ya shiga cikin kakanninsa. 

"Abin takaici shi ne saboda ya bar babban gibi a rayuwarmu, da jiharmu, da ma Najeriya baki daya. Duk da haka, muna farin ciki da cewa Kabiyesi ya yi rayuwa mai tsawo." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN