Duba abin da ya faru bayan jirgin sama na sojin Najeriya NAF ya fado daga sararin samaniya


Ana fargabar cewa jami'an hukumar sojin saman Najeriya NAF sun mutu a wani hatsarin jirgin da ya afku a ranar Talata a jihar Kaduna.

Har yanzu babu cikakken bayanin yannadda lamarin ya auku. 

Duk da haka, TheCable ta fahimci cewa lamarin ya shafi wani jirgin sama na horo wanda ke da matukan jirgi biyu.

Wannan lamarin ya faru ne watanni 11 bayan da jirgin NAF ya yi hatsari a Kaduna.

Lamarin, wanda ya faru a watan Mayun 2021 , ya hada da Beechcraft 350, kuma jirgin ya yi hatsari a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.

Ibrahim Attahiru, babban hafsan soji, da wasu jami’an soji 10 da ke cikin jirgin a lokacin da jirgin ya fadi, sun mutu.

An ce Attahiru na kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ne domin halartar wani faretin yaye sabbin hafsoshin soji da suka kammala samun horo.

Bayan faruwar lamarin, ‘yan majalisar marasa rinjaye a majalisar wakilai sun bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa an gudanar da bincike mai zurfi a kan irin wannan lamari da ya shafi jiragen soji a kasar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN