Dan wasan Manchester United Bruno Fernandes ya yi hatsarin mota gabanin wasan Liverpool (hotuna)


Dan wasan tsakiya na Manchester United, Bruno Fernandes ya yi hatsarin mota a ranar Litinin din da ta gabata amma ya tsallake rijiya da baya.

Dan wasan tsakiya na Portugal bai ji rauni ba bayan lamarin da ya shafi Porsche kusa da sansanin horo na kungiyar na Carrington - kuma ana sa ran zai yi atisaye kamar yadda ya saba a yau. An kuma yi imanin cewa sauran bangarorin da suka yi karon ba su ji komai ba. 

Hotunan da lamarin ya afku sun nuna motar - da kudinta ya kai fam 90,000 - ta lalace a gefen direban, inda motoci biyu suka garkame a kan wata siririyar hanya.An kuma ga jami’an agajin gaggawa a wurin da hadarin ya auku.

Mai yiwuwa kocin rikon kwarya na United Ralf Rangnick zai ba da cikakken bayani kan yanayin dan wasan a taron manema labarai da zai yi kafin wasan da yammacin yau.  


Hadarin Fernandes na zuwa ne kwana guda gabanin wasan da kungiyarsa ta buga da Liverpool a gasar Premier.

Tauraron dan wasan ya kasance muhimmin dan wasa a kungiyar tun lokacin da ya koma Manchester United daga Sporting Lisbon a watan Janairun 2020. Ya zura kwallaye 49 a wasanni 120 da ya buga. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN