An yi garkuwa da wata matashiya mai suna Tina Moses rana Jajibir na daurin aurenta a jihar Kaduna.
A ranar Asabar 16 ga watan Afrilu ne aka shirya za a daura auren matar da angonta Elisha Koje a karamar hukumar Sanga da ke jihar.
A cewar Esther Attah Asheri, yar uwarta, Tina an yi garkuwa da ita ne a ranar Juma’a a kan hanyarta ta zuwa salon gyara gashi a garin Kaduna.
“An yi garkuwa da surukata a garin Kaduna a yau ya kamata a ce ranar farin cikinmu ne domin a yau za ta bi hanya amma wasu sun gwammace su sanya ranar bakin ciki a gare mu baki daya, don Allah a hada mu da mu yi mata addu’a domin ta dawo lafiya."
Esther ta kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan amma har yanzu basu nemi kudin fansa ba.