Da dumi-dumi: An harbe jami'in INEC a Imo har Lahira, duba yadda ta faru



An harbe Mista Nwokorie Anthony, jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Imo.

An kashe jami’in ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a (CVR) a karamar hukumar Ihitte Uboma da ke jihar.

A cewar Kwamishinan Zabe (REC), Farfesa Emeka Ezeonu, an kashe Nwokorie ne a Nkwo Ihitte (PU 004) da ke Amakohia Ward (RA 02) na karamar hukumar Ihitte Uboma, yayin da ba a san inda wasu ma’aikatan biyu da ke aikin rajistar su ke ba. .

A bisa wannan mumunan lamarin hukumar zabe ta dakatar da gudanar da atisayen a karamar hukumar.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

“Kafin faruwar lamarin, hukumar ta dakatar da CVR a kananan hukumomin Osu da Njaba na jihar saboda rashin tsaro yayin da ake gudanar da atisayen a ofishin karamar hukumar INEC a Oru Gabas, Oru ta Yamma, Orlu da Ohaji-Egbema.”

“Hukumar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan Nwokorie Anthony tare da addu’ar Allah ya basu ikon jure rashin. An kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro domin bankado wadanda suka haifar da wannan mummunan lamari tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya,” inji Okoye.

Ya bukaci shugaban kungiyar garuruwa daban-daban na jihar Imo da kuma masu ruwa da tsaki da su kare ma’aikatan hukumar da ke gudanar da ayyukan kasa.

Ya ce, “Kiyaye da tsaron ma’aikatan na da matukar muhimmanci ga hukumar, musamman yadda aikin rajistar masu zabe ya wuce ofisoshin jahohinmu da na kananan hukumomin kasar nan, a kokarinmu na yiwa ‘yan Najeriya hidima.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN