Alamomi 12 na shugaba mai yin tsafi domin harkar mulki - Tubabben dan Tsibbu


Wani dan Tsibbu da ya ce ya tuba mai suna Dan Ado, ya yi bayani yadda wasu masu neman mulki ko shugabanci ke hadawa da tsafi, tsibbu da sauran makaru komabayan ikon Allah kawai domin neman biyan bukatarsu ta Duniya. Shafin isyaku.com ya tattaro.

Dan Ado ya ce wasu daga cikin halaye da za ka kula cewa shugaba ko mai mulki yana kaucewa hanyar Allah zuwa ga tafarkin tsafi da tsibbu sun hada da

1. Kyamar talaka bayan ya kai ga mukami ko shugabanci.

2. Duk wanda ya wahala da shi kafin ya kai ga shugabanci, mulki ko mukami, zai mayar da shi makiyi karfi da yaji.

3. Kin taimaka wa wadanda suka taimaka masa lokacin da yake neman shugabanci ko mulki bayan ya sami shugabanci.

4. Saka wa wadanda suka yi adawa da shi da alhairi ta hanyar basu mukamai ko biya masu bukatu nan take idan suka zo da wata bukata.

5. Mayar da masoyansa su koma makiyansa da gangan.

6. Raina Sarakuna, Malaman addini da Dattijai masu kima a cikin al'umma. Ba wanda ya isa ya ba shi shawara akan sha'anin mulki ko shugabancin al'umma .

7. Yawan yi wa talakawansa karya.

8. Rashin jin kunyan talaka ko da an zarge shi da yin satar dukiyar talaka ko zubewar mutunci.

8. Yawan cin mutuncin talaka wajen harkar mulki ko shugabanci.

9. Yawan neman Matan banza ko yi Luwadi. 

10. Mayar da talaka abin fadansa.

11. Yin gaba da talaka.

12. Dagewa tukuru domin ganin bayan talaka

Dan Ado ya ce wadannan wasu ne daga cikin abubuwan da ake yin sharadi da mutum cewa zai yi kafin a yi masa aikin tsafi ko tsibbu, kuma su ne ginshikin nassarar da dorewar shugabanci ko mulkinsa idan yana son kar makiya ko mahassadansa su yi galaba a kanshi inji bacewar tafarkin tsafi da tsibbu.

Za mu dakata a nan daga firar da Dan Ado ya yi da mu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN